Isa ga babban shafi
Amurka

Ya kamata a karrama ni da kyautar Nobel - Trump

Shugaban Amurka Donald Trump, ya bayyana rashin karrama nasaorin da ya cimma a matsayin daya daga cikin damuwar da yake da ita, kan Majalisar Dinkin Duniya. 

Shugaban Amurka Donald Trump tare da mai dakinsa Melania.
Shugaban Amurka Donald Trump tare da mai dakinsa Melania. REUTERS/Tom Brenner
Talla

Trump ya ce abin takaici ne yadda majalisar dinkin duniyar ta hana shi kyautar lambar da ake baiwa mutanen da suka yi fice.

Shugaban na Amurka ya kara da cewar yana da yakini ana iya bashin wannan lambar girma ta fannoni da dama, muddin akwai adalci wajen bada lambar girmar, wanda kowa ya san ba haka suke yi ba.

Trump yace Majalisar ta baiwa shugaba Barack Obama lambar girma lokacin da yah au karagar mulki, amma shi ya duba bai ga dalilin bashi lambar girmar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.