rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Birtaniya Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kotu ta soke kudirin rufe majalisar Birtaniya

media
Borris Johnson Firaministan Birtaniya Jeff Overs/via REUTERS

Babban kotu a birnin Landan ta soke kudirin Firaministan kasar Borris Johnson na dakatar da zaman majalisar dokokin kasar.Kotun a zaman ta na yau ta bukaci yan Majalisar su gaggauta komawa aikin su.


Yan lokuta da daukar  mataki  dakatar da aikin Majalisa daga Firaministan kasar Borris Johnson, dubban ‘yan Birtaniya suka gudanar da zanga-zanga a sassan kasar, don nuna adawa da matakin Fira Minista Boris Johnson, na dakatar da aikin majalisar kasar har sai ya rage makwanni biyu su fice daga cikin kungiyar tarayyar Turai, ranar 31 ga watan Oktoba.

Da daukar wannan mataki, bangaren ‘yan adawa sun kalubalanci matakin na Fira Minista Boris Johnson a kotu.

A baya bayan nan Fira Minista Boris Johnson yayi gargadin cewa ba zai lamunci duk wani yunkuri daga wasu ‘yan majalisar kasar ba, da suka daura aniyar dakatar da ficewar Biraniya daga daga cikin kungiyar turai, ko kuma tsawaita wa’adin kammala rabuwarsu na ranar 31 ga watan Oktoba.

Johnson ya ce muddin ‘yan majalisun kasar suka cimma nasarar aiwatar da wannan aniya, to fa ba shakka ‘siyasar Birtaniya za ta rasa kima da amincewa daga yan kasar, la’akari da cewa sun ne suka zabi ficewa daga cikin kungiyar kasashen Turai a shekarar 2016.