rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Emmanuel Macron

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Zai yi wuya Faransa ta ci gaba da bayar da mafaka - Macron

media
Shugaban Faransa Emmanuel Macron yayin jawabinsa a taron Majalisar Dinkin Duniya REUTERS/Carlo Allegri

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa, ya ce kasar ba za ta iya bai wa kowa mafaka ba, matukar za ta duba cikakkiyar cancanta kafin karbar tarin bakin hauren da ke tururuwar shigarta daga sassa daban-daban.


Shugaba Macron wanda ke wannan batu, yayin taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya a New york na kasar Amurka, ya ce karkashin tsarin tsaurara matakan bayar da mafaka, abu ne mai wuya Faransar ta ci gaba da bayar da mafaka.

Karkashin tsarin da Macron ya gabatar a makon jiya na tsaurara matakan bayar da mafakar musamman yanzu a tsakiyar wa’adinsa, ya ce babu hanyar samun mafaka a Faransar matukar suna fatan karbar mutane yadda ya kamata.

A cewarsa bayan gabatar da shirin tsaurara matakan bayar da mafakar babu bukatar ci gaba da kada kuri’a kan batun don dadadawa masu tsatsauran ra’ayi dai dai lokacin da zaben kasar ke tunkarowa.

Cikin jawabin na shugaba Macron, ya ce Faransa ta fuskanci yawaitar masu neman mafaka tun daga shekarar 2017, tun bayan da gwamnatinsa ta sha alwashin bayar da cikakkiyar kulawa ga ‘yan cirani, sai dai ya ce kasar ba ta samu goyon bayan kasashen Turai kamar yadda ya kamata wajen wanzuwar aikin ba.

Jawabin na shugaba Emmanuel Macron na zuwa ne a dai dai lokacin da ya rage mako guda Majalisar kasar ta bayar da damar tafka muhawara kan sabon tsarin shige-da-fice a kasar.

Matakin Macron wanda wa’adinsa zai kare a shekarar 2022 ana ganin baya rasa nasaba da yadda babbar abokiyar dabinsa Marine Le Pen da Jam’iyyar ta masu tsattsauran ra ‘ayi ta yi kaurin suna wajen kyamar baki, wanda kuma za ta iya yi masa fintinkau da tsarin yayin zaben kasar mai zuwa.