rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Nicolas Sarkozy

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kotun Faransa ta yi watsi da bukatar Sarkozy kan janye tuhumarsa

media
Tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy. Handout / AFP

Kotu a Faransa ta yi watsi da daukaka karar tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarcozy da ke neman dakatar da umarnin gurfanar da shi gaban kotu, domin fuskantar tuhuma kan laifin yin amfani da kudaden gwamnati yayin yakin neman zabensa a shekarar 2012.


Sarkozy wanda tuni ya ke fuskantar shari’a kan zargin bai wa alkali cin hanci, zai fuskanci karin tuhumar ce kan zargin amfani da kudaden da suka ninka adadin da doka ta kayyade sau biyu, wajen yakin neman zabensa.

Matakin Kotun kan Sarkozy na zuwa a dai dai lokacin da tsohon Firaministan kasar  Eduard Balladur zai gurfana gaban kotu don fuskantar tuhuma kan aikata badakala a wani cinikin makamai da Pakistan.

Mahukuntan kasar na zargin Eduard Balladur da amfani da kudaden da aka samu wajen yakin neman zaben shugaban kasa da bai yi nasara ba a shekarar 1995.