rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Wani mahari ya kashe 'yan sandan Faransa da wuka

media
An killace ginin shalkwatan 'yan sandan Faransa bayan harin wuka da ya kashe jami'ansu hudu. Martin BUREAU / AFP

Wani mahari ya kashe jami’an ‘yan sandan Faransa a shalkwatansu da ke birnin Paris bayan ya far musu da wuka kafin daga bisani a bindige shi har lahira.


Mai shigar da kara na birnin Paris, Remy Heitz ya ce, maharin mai shekaru 45, na aiki ne tare da sashin sadarwar fasaha da musayar bayanan sirri a shalkwatan ‘yan sandan .

Maharin ya kashe jami’an ‘yan sanda uku da suka hada da mace guda da kuma wani ma’aikaci daban, yayin da Ministan Harkokin Cikin Gidan Faransa, Christophe Castaner ya ce, tun shekarar 2003 ne maharin ke aiki da jami’an ‘yan sandan.

Ministan ya ce, maharin bai taba nuna wata alamar mummunar dabi’a ba a can baya.

Tuni aka katange ginin shalkwatan ‘yan sandan da ke kusa da shahararriyar mujami’ar Notre Dame bayan aukuwar wannan lamarin.

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya ziyarci shalkwatan, yayin da tuni aka fara gudanar da bincike a gidan maharin domin samun wasu boyayyun bayanai.