rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Jamus

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan bindiga sun kashe mutane a Jamus

media
Jami'an tsaron Jamus na cikin shirin ko-ta-kwana a birnin Halle bayan harin 'yan bindigan da suka kashe mutane biyu REUTERS/Marvin Gaul

Jami’an tsaron Jamus sun cafke mutun guda da ake zargi da hannu a harin bindigar da ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla biyu a birnin Halle, yayin da aka bukaci jama’ar yankin da su ci gaba da zama a gida.


A sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter, rundunar ‘yan sandan Jamus ta ce, jami’anta sun kama daya daga cikin maharan a daidai lokacin suke kan farautar su bayan tserewarsu.

‘Yan bindigan sun tsere a cikin mota jim kadan da bude wutar a gaban wata majami’ar Yahudawa da ke gundumar Paulus, yayin da kuma suka cilla wa makabartarsu bam kirar gida kamar yadda jaridar Bild ta rawaito.

Rahotanni sun ce, daya daga cikin maharan na sanye ne da kakin soji baya ga dimbim makamai da yake dauke da su.