rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Ecuador Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Masu zanga-zanga sun yi watsi da tayin ganawa da shugaban kasa

media
Masu zanga-zangar kin jinin gwamnati kan cire tallafin mai a Ecuador. REUTERS/Ivan Alvarado

Jagororin masu zanga-zangar kin jinin gwamnati a Ecuador, sun yi watsi da tayin tattaunawar kai tsaye da shugaban kasar Lenin Moreno.


Masu zanga-zangar da suka shafe sama da kwanaki 10 suna bore, sun gindaya sharadin tilas gwamnatin ta janye matakin cire tallafin man fetur da ta dauka, kafin shiga tattaunawar sulhu.

A baya bayan nan masu zanga-zangar suka yi garkuwa da jami’an ‘yan sandan kasar 8, a dai dai lokacin da boren da dubbansu ke yi ya kazanta, kan adawa da matakin tsuke bakin aljihun gwamnati da kuma cire tallafin man fetur.

Kawo yanzu mutane 5 suka rasa rayukansu bayan shafe sama da mako guda suna bore, abinda ya tilastawa fadar gwamnati yin hijira daga babban birnin kasar Quito.