Isa ga babban shafi
Brexit

Brexit: Ana iya cimma yarjejeniya a wannan mako - Barnier

Babban mai shiga tsakani kan ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai Michel Barnier, ya ce ana iya cimma yarjejeniyar rabuwar a wannan mako, amma yayi kashedin cewa akwai sarkakiya da dama da ake bukatar warware wa.

Michel Barnier
Michel Barnier Photo: Emmanuel Dunand/AFP
Talla

Jami’en Birtaniya da na Turai na ta ribibin cimma yarjejeniya kafin babban taron jagororin nahiyar da za a fara ranar Alhamis, yayin da Firaminista Boris Johnson ke kokarin cika alkawarinsa na fitar da Birtaniya daga kungiyar Tarayyar Tuarai a ranar 31 ga watan Oktoba.

Da saukar sa Luxembourg don yin bayani ga kasashen kungiyar Turai 27 kan tattaunawar sirri da suka yi, Barnier ya bayyana kwarin gwiwar cimma yarjejeniya, amma kuma yana kaffa- kaffa.

"Muna ta aiki tukuru tun a karshen makon da ya gabata da jiya, saboda duk da cewa akwai sarkakiya game da yarjejeniyar, akwai yiwuwar cimma yarjejeniya a wannan mako.’’ In ji Barnier.

"A bayyane yake, dole yarjejeiyar ta yi wa kowa dadi – da Birtaniya da ma Tarayyar Turai."

Bayan makonnina fargabar cewa Birtaniya naiya ficewa daga Turaiba yarjejeniya, akwai dan alamun cewa ana iya kai ga gaci a tattaunawar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.