Isa ga babban shafi
Faransa

Kotun Faransa ta daure mata 'yan jihadi a gidan yari

Kotun Faransa ta daure wasu mata ‘yan jihadi shekaru 5 zuwa zuwa 30 a gidan yari sakamakon yunkurinsu na tayar da bam a harabar katafariyar majami’ar Notre Dame.

Wata mace da aka zarga da zama daya daga cikin mayakan jihadi a Faransa
Wata mace da aka zarga da zama daya daga cikin mayakan jihadi a Faransa Ammar Karim / AFP
Talla

Wannan ita ce shari’a ta farko da ta shafi gungun mata da ke yunkurin kai hari a kasar Faransa wadda fara gamuwa da farmakin ‚yan ta’adda tun shekarar 2015, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 255.

An kama matan su 5, masu shekaru tsakanin 22 zuwa 42 a wata mota jibge da tukwanen iskar gas kusa da cocin na Notre Dame a watan Nuwamban shekarar 2016.

Biyu daga cikin matan, Ines Madani da Ornella Gilligmann, sun bade motar da man diesel a tsakiyar dare, kuma suka yi kokarin cinna mata wuta da sigari amma abin ya ci tura.

An yi amanna cewa, matan na aiki ne da umurnin Rachid Kassim, wani Bafaranshe mai taimaka wa kungiyar IS wajen farfaganda, wanda kuma ake zargi da umurtar kisan wani dan sandan Faransa a watan Yunin shekarar 2016.

Rahotanni sun ce, ana ganin an kashe Kassim a wani harin da aka kai ta sama a birnin Mosul na Iraqi a watan Fabrairun 2017.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.