Isa ga babban shafi
Birtaniya

Birtaniya da EU sun cimma sabuwar yarjejeniyar Brexit

Birtaniya da Kungiyar Tarayyar Turai sun sanar da cimma kudirin yarjejeniyar ficewar kasar wanda ya yanzu haka ke dakon amincewar mambobin majalisar dokokin kasar da ta kungiyar EU.Tuni shugabannin kasashen Turai da ‘yan siyasa suka fara mayar da martani kan wannan matsaya.

Shugaban hukumar Tarayyar Turai  Jean-Claude Juncker tare da Firaministan Birtaniya Boris Johnson
Shugaban hukumar Tarayyar Turai Jean-Claude Juncker tare da Firaministan Birtaniya Boris Johnson REUTERS
Talla

Shugaban Hukumar Tarayyar Turai, Jean Claude Juncker ya yi marhabin da yarjejeniyar, yana mai fatan cewa, ba za a sake jinkirta ficewar Birtaniya nan gaba ba.

Shi kuwa mai shiga tsakani na EU kan batun na Brexit, Michel Banier cewa, ya ce, sun samar da sabuwar mafita a dokance domin magance batun tsattsauriyar iyaka da kuma tabbatar da zaman lafiya a tsibirin Ireland.

Sai dai ya bukaci a yi taka-tsan-tsan, lura da cewa, dole ne a gabatar da wannan kudirin yarjejeniyar ga majalisar dokokin Birtaniya wadda a can baya ta yi fatali da yarjejeniyoyi uku da aka cimma.

A sakon da ya aika ta kafar Twitter, Firaministan Birtaniya, Boris Johnson ya yi fatan cewa, yanzu dai ‘yan majalisar za su amince da wannan yarjejeniya.

A bangare guda, Jam’iyyar DUP ta arewacin Ireland da gwamnatin Johson ta dogara da ita wajen samun goyon bayanta a majalisar dattawan Birtaniya, ta ce, ko kadan ba za ta amince da kudirin ba.

Kazalika shugabar Jam’iyyar National Party ta Scotland, Nicola Sturgeon ta ce, ba za su kada kuri’ar amincewa da yarjejeniyar ba.

Shi ma shugaban jam’iyyar adawa ta Labour a Birtaniya, Jeremy Corbyn ya bukaci mambobin majalisar da su yi watsi da yarjejeniyar, yayin da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce, yana da kwarin guiwar cewa, majalisar Biraniyar za ta amince da wannan yarjejeniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.