rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Spain Catalonia

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Zanga-zangar Catalonia ba barzanar rikidewa zuwa bore

media
Magoya bayan 'yan aware a yankin Catalonia. AFP

A wannan Juma'a alummar yankin Catalonia dake Spain suka tsunduma yajin aikin gama gari, inda aka shafe tsawon kwanaki ana zanga-zanga kan bukatar ballewar yankin daga kasar.


Dubban mutane ne suka taru a birnin Barcelona domin adawa da daure 9 daga cikin ‘yan aware kuma tsaffin shugabannin yankin na Catalonia.

A yayin da fusatattun magoya bayan jagororin ‘yan awaren ke cika kwanaki biyar da soma zanga-zangar, masu fafutuka sun tare hanyoyi da dama a arewa maso yammacin yankin, da ya raba su da kan iyakar kasar da Faransa.

Ma’aikatan kasar sun nuna rashin amincewarsu da hukuncin daurin shekaru 13 a gidan yari da kotun kasar ta yankewa shugabannin ‘yan awaren, wadanda basu yi nasara a yunkunrinsu na ballewa daga Spain ba.

Duk da yajin aikin da ke gudana, dubban mutane sun kwarara cikin Barcelona, bayan shafe kwanaki 3 suna tattaki a garuruwa biyar dake yankin Catalonia, da zummar tada tarzoma a hanyoyin da suka kasance masu muhimmanci a Spain.