rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Birtaniya Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

EU na zama na musamman kan zaben Birtaniya gabanin Brexit

media
Firaministan Birtaniya Boris Johnson a gaban kungiyar Tarayyar Turai Reuters

Dai dai lokacin da Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya bukaci gudanar da zaben gaggawa a kasar ranar 12 ga watan Disamba, shugabannin kungiyar Tarayyar Turai, na shirin wata ganawa ta musamman kan bukatar Birtaniya na sake tsawaita mata wa’adin ficewa daga kungiyar.


Galibin kasashen EU na fatan girmama bukatar ta Birtaniya kan kara mata wa’adin watanni 3 bisa sharadin gaggauta ficewa matukar majalisar kasar ta amince da sabuwar yarjejeniyar EU da Johnson suka cimma cikin watan nan.

Sai dai a bangare guda Faransa na kalubalantar matakin tare da fatan karkare komi a wa’adin farko da aka dibarwa kasar na ranar 31 ga watan nan na Oktoba.

Firaminista Boris Johnson ya bai wa Majalisar kasar zabin su goyi baya ga matakinsa na kiran zaben gaggawa a ranar 12 ga watan Disamba, shi kuma ya basu cikakkiyar damar tafka muhawara kan sabuwar yarjejeniyar tasa.

A cewar Johnson Birtaniya za ta tsawaita ficewa daga EU ne kadai idan Majalisar kasar ta mara baya ga matakinsa na fatan gudanar da zabe a watan Disamba, yayinda shi kuma zai tsawaita ficewar zuwa watan Janairu.