rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Birtaniya Vietnam

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Direban da ya dauko gawarwaki na fuskantar tuhume-tuhume 39

media
Wurin da aka gano gawarwakin mutane 39 makare a cikin akwatin katuwar mota a Birtaniya AFP/File / Ben STANSALL

‘Yan sandan Birtaniya sun gabatar da jerin tuhume-tuhume sama da 30 kan Maurice Robinson, direban motar da aka gano gawarwakin mutane 39 cikinta.


Robinson na fuskantar tuhume-tuhumen da suka kunshi, kisan kai, safarar mutane, da kuma hallata kudaden haramun.

Cikin makon da ya kare aka kame direban mai shekaru 25 dan arewacin Ireland, jim kadan bayan gano gawarwakin da suka hada da na mata 8 da maza 31, da ake kyautata zaton cewar ‘yan kasar Vietnam ne, a wani yankin masana’antu dake kudu maso gabashin Ingila.

Gurfanar deriban na zuwa ne yayinda iyalai da dama a kasar Vietnam suka bayyana fargabar kasancewar ‘yan uwansu da suka bace cikin gawarwakin da aka gano.