rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa Gasar Cin Kofin Turai UEFA Ingila Bulgaria

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

UEFA ta tilastawa Bulgaria biyan tarar dala dubu 83

media
Bulgaria za ta biya tara mai tsoka, gami da buga wasa ba tare da 'yan kallo ba, saboda rashin da'ar magoya baya. AFP/File / NIKOLAY DOYCHINOV

Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai UEFA, ta yanke hukuncin tilastawa Bulgaria biyan tarar dala dubu 83, kwatankwacin naira miliyan 29 da dubu 921, da 500, sai kuma buga wasan neman tikitin zuwa gasar cin kofin nahiyar Turai ba tare da yan kallo ba.


Hukuncin na UEFA ya biyo bayan yadda wasu magoya bayan kasar ta Bulgaria suka rika furta kalaman cin zarafi da nuna wariyar launi, ga ‘yan wasan kasar Ingila, yayin fafatawarsu a wasan neman cancantar zuwa gasar kwallon kafar kasashen Turai ta 2020 a farkon wannan wata na Oktoba.

Yayin wasan dai Ingila ta lallasa Bulgarian ne da kwallaye 6-0 ranar 14 ga watan Oktoban da muke ciki.

Hukuncin ladabtarwar na nufin Bulgaria za ta fafata tsakaninta da Jamhuriyar Czech a gida ranar 17 ga Nuwamban dake tafe ba tare da ‘yan kallo ba.

A gefe guda kuma hukumar ta UEFA, ta ce tilas hukumar kwallon kasar ta Bulgaria ta biya tarar euro dubu 10, kwatankwacin naira miliyan 4 a matsayin nata kashin na ladantarwar, domin tsawatarwa magoya bayan kwallon kafarsu a nan gaba kan laifin nuna wariyar launi.