Isa ga babban shafi
Turkiya-Turai

Turkiya ta soma tasa keyar mayakan IS zuwa kasashensu

Yau litinin Turkiya ta fara tasa keyar mayakan IS ‘yan kasashen waje mafi akasari daga yankin Turai zuwa kasashen su na asali, ciki har da Faransawa, da kuma Jamusawa.

Turkiya ta soma cika alkawarin mayar da mayakan IS da ta kama zuwa kasashensu na asali.
Turkiya ta soma cika alkawarin mayar da mayakan IS da ta kama zuwa kasashensu na asali. AFP
Talla

Tun ranar Juma’ar da ta gabata ne dai Turkiya ta sha alwashin cewar za ta soma mayar da mayakan IS da ke hannunta zuwa kasashensu na asali.

Gabanin sanarwar, ministan cikin gidan Turkiyan Suleyman Soylu, yace yanzu haka, kasar na tsare da mayakan kungiyar ta IS kusan dubu 1 da 200, banda karin wasu 287 da ta kame, yayin farmakin baya bayan data kaddamar kan mayakan Kurdawa a arewacin kasar Syria.

Turkiya dai ta dade tana sukar kasashe da dama, musamman na yammacin Turai, da kin karbar ‘ya ‘yansu da suka zama mayakan IS a Syria da Iraqi, inda suke soke damar kasancewarsu ‘yan kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.