Isa ga babban shafi
Faransa

Tarzoma ta barke a bukin ciki shekara 1 da soma zanga-zangar Faransa

A Faransa tarzoma ta barke tsakanin ‘yan sanda da masu riguna Dorawa da suka soma zanga-zangar tunawa da cika shekara daya da adawa da wasu manufofin shugaba Emmanuel Macron. 

Masu zanga-zangar rigunan dorawa a Faransa, yayin arrangama da jami'an tsaro.
Masu zanga-zangar rigunan dorawa a Faransa, yayin arrangama da jami'an tsaro. AFP/Geoffroy van der Hasselt
Talla

A wasu anguwannin birnin Paris, ‘yan sanda sunyi amfani da hayaki mai sa kwalla, sakamakon barnata kaddarori da masu zanga-zangar suka so yi, lamarin da ya kai ga kame gomman su a cewar rahotanni.

A wannan lahadi ake cika shekara guda da soma zanga-zangar ta masu sanye da rigunan dorawar, wadanda suka soma kalubalantar manufofin gwamnatin shugaba Emmanuel Macron kan tattalin arziki, a ranar 17 ga Nuwamban shekarar bara.

A ranar faron dai kusan mutane dubu 300 suka shiga zanga-zangar data rika gudana a kowane mako, gami da yin arrangama da jami’an tsaro, sai dai sannu a hankali adadin mutanen dake fita ya ragu matuka zuwa kasa da dubu 20.

Gwamnatin Macron ta soma fuskantar gagarumin kalubalen ne, bayan zartas da karin farashin albarkatun mai da wasu sauye-sauyen da ta bayyana a matsayin shirin karfafa tattalin arzikin kasar, lamarin da ya haddasa zanga-zanga a sassan kasar da ta juye zuwa tarzoma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.