Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa za ta yi wa masu cin zarafin mata hukunci mai tsauri

A daidai lokacin da Duniya ke bikin ranar yaki da cin zarafin mata, gwamnatin Faransa ta kaddamar da wasu sabbin matakai da za su magance cin zarfin da matan ke fuskanta ta hanyar kisa ko kuma nakasa su bayan da a yanzu kasar ke matsayin jagaba wajen yawaitar kisan mata.

Shugaban Faransa  Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron Ludovic Marin/Pool via REUTERS
Talla

Yayin gabatar da jawabi a daidai lokacin da bukukuwan ranar yaki da cin zarafin mata ke ci gaba da gudana a sassan duniya, Firaministan Faransa Edourd Phillippe ya ce akwai sabbin matakai da za su magance matsalar.

Matan Faransawa dai su ne kan gaba da ke fuskantar cin zarafi ta hanyar kisa ko jikkatawa daga tsaffin mazajensu ko samarinsu koma mazajen da su ke tare da su.

A cewar Philippe sabbin matakan za su karfafa hukuncin da za a rika zartaswa wadanda aka samu da makamantan laifin baya ga samar da cikakkiyar kariya ga mata.

Kalaman Firaministan na Faransa dai na zuwa ne kwanaki 2 bayan kakkarfar zanga-zangar da dubbunnan mata suka gudanar a biranen kasar don nuna damuwa da halin da mata ke fuskanta gabanin fara bukukuwan ranar yaki da cin zarafin matan a duniya bisa bukatar Majalisar Dinkin Duniya.

Rahotanni sun bayyana cewa daga watan Janairun shekarar nan zuwa yanzu akalla mata 117 tsaffin mazajensu ko kuma samarinsu suka hallaka a fadin kasar ta Faransa, sama da adadin mata 121 da aka hallaka a bara.

Ka zalika wani rahoto na daban ya nuna cewa kowacce shekara mata dubu 213 ke fuskantar cin zarafi da suka kunshi ko dai kisa ko fyade ko kuma jikkatawa daga tsaffin mazaje ko samarinsu a sassan duniy

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.