Isa ga babban shafi
Faransa

Ta hanyar siyasa ce za a warware rikicin Sahel - Faransa

Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian, ya ce akwai bukatar gwamnatocin Mali da kuma Burkina Faso su dauki matakai na siyasa domin samar da zaman lafiya a cikin kasashensu, tare da rage karfin ayyukan ta’addanci.

Shugaban Faransa  Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron LUDOVIC MARIN / AFP
Talla

Le Drian dai na magana ne gaban kwamitin harkokin waje na majalisar dokokin Faransa wanda ke neman karin haske dangane da mutuwar sojojin kasar 13 a Mali.

Ministan harkokin wajen ya ce akwai bukatar mahukunta a Mali su kara daukar sabbin matakai na siyasa tare da mutunta alkawulla da kasar ta dauka wa kungiyoyin da ke dauke da makamai a yarjejeniyar a birnin Algers na kasar Algeria a 2015.

Le Drian ya ce wannan yarjejeniya ce ta tanadi yadda za a kwance damarar mayakan da ke dauke da makamai da kuma bai wa yankunan kasar karin cin gashin kai, yana mai cewa ta hakan ne kawai gwamnatin Mali za ta samu damar aika wakilanta a yankin Kidal.

Ministan na harkokin wajen Faransa ya kara yin kira ga kasashen duniya da su cika alkawarin da suka dauka na taimakawa rundunar samar da tsaro ta G5-Sahel da kudade da yawansu ya kai Euro milyan 414, inda kawo yanzu milyan 176 kawai ne suka shiga hannu.

Wani lokaci a baya, ministar tsaron Faransa Florence Parly ta ce har yanzu kasar Saudiyya ba ta bayar da Euro milyan 100 da ta yi alkawarin bai wa rundunar ta G5-Sahel ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.