Isa ga babban shafi
Jamus-Rasha

Jamus ta kori jami'an Diflomasiyyar Rasha 2 kan zargin kisan kai

Gwamnatin Jamus ta kori jami’an Diflomasiyyar Rasha guda 2 bayan ikirarin masu shigar da kara da ke ganin Moscow na da hannu a kisan jagoran ‘yan tawayen Chechenia Zelimkhan a Berlin.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel.
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel. 路透社
Talla

A ranar 23 ga watan Agustan da ya gabata ne, wani da ake zargin dan Rasha ne ya harbe Zelimkhan Khangoshvili kwamandan ‘yan tawayen Chechenia har lahira a Berlin, wanda kuma nan take jami’an tsaron Jamus suka kame shi yayinda kuma binciken baya-bayan nan ke nuna cewa Rasha ke da hannu wajen bayar da umarnin kisan kwamandan.

Kisan Zelimkhan na matsayin kari kan tsamin alakar Rasha da Jamus bayan zargin yunkurin kisan Sergei Skripal a bara, tsohon jami’in leken asirin Rashan da ya koma aiki da Birtaniya, zargin da ya haddasa korar jami’an Diflomasiyya daga bangarori daban-daban.

Bayan matakin na Jamus a yau Laraba, ma’aikatar harkokin wajen Rasha ta fitar da sanarwar cewa nan gaba kadan za ta sanar da matakin dauka kan Jamus.

Ka zalika Rashan ta zargi Jamus da siyasantar da lamarin tana mai cewa mataki da bazata amince da shi ba.

Rahotanni daga Jamus sun bayyana cewa mutumin da ake zargi da kisan yana haye ne akan keke lokacin faruwar lamarin kuma bayan ya harbe Zelimkhan ne ya jefa keken da sauran bindigoginsa a ruwa amma kuma jami’an tsaro suka yi nasarar kama shi lokacikankani bayan faruwar lamarin.

Makashin wanda jami’an tsaron Jamus suka bayyana sunanshi da Vadim S wasu bayanai na nuni da cewa yana amfani da sunan karya haka zalika bayanai.

Cikin sanarwar sallamar jami’an Diflomasiyyar na Rasha, Jamus ta bayyana cewa Moscow ta gaza bayar da hadin kan da ake bukata wajen gudanar da bincike inda ta mika binciken ga sashen fikira.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.