Isa ga babban shafi
Faransa

An soma yajin aikin gama - gari a Faransa

Faransa ta tsunduma cikin wani gagarumin yajin aiki a yau alhamis, musaman banaren kungiyoyin kwadagon sufurin jiragen kasa, domin tilasta shugaba Emmanuel Macron ya ci tuwon fashi kan shirinsa na samar da sauye sauye a fannonin fanshon da na  ritaya

Shugaban Faransa  Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. REUTERS/Henry Nicholls
Talla

Yau da yan kwanaki da suka gabata, maganar yajin aikin ce ta mamaye jaridun kasar, tare kuma da maida shi abin tattaunawa a bakunanan al’umma suna tambayar juna yadda zasu kwashe da wannan rana ta yau alhamis

Yajin aikin na yau da za a iya kwashe tsawon kwanaki ana gudanarwa, a dayan biyu yake, ko dai ya tsoratar ko kuma faranta ran faransawa.

Abinda ke cikin tunanin faransawa dai shine, tuni da zanga zangar al’umma da aka gudanar a 1995 da ta rukusar da kasar na kusan wata guda, tare da tilastawa gwamnatin ja baya kan matakinta na sauya tsarin ritayar a kasar

Kungiyoyin kwadagon sun ce kashi 90 na jiragen kasar dake zirga zirga a fadin kasar yau ba za suyi aiki ba, yayin da za’a dakatar da aikin daukacin jiragen dake jigila a cikin birin Paris da soke tashi da saukar daruruwan jiragen sama da rufe akasarin makarantun kasar.

Rahotanni sun ce yajin aikin na iya daukar kwanaki, kuma yanzu haka ana kwatanta shi da irin wanda akayi a shekarar 1995 wanda ya dauki makwanni 3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.