Isa ga babban shafi

Tsauni mai aman wuta ya halaka mutane da dama a New Zealand

‘Yan Sandan New Zealand, sun ce babu wani karin mutum da ake sa ran cetowa da rai, daga wani tsibiri a kasar da tsauni yayi aman wutar bazata a yau litinin, yayinda kuma suka ce sama da mutane 20 ake fargabar sun halaka.

Tsibirin White Island a kasar New Zealand, inda tsauni yayi aman wuta na bazata.
Tsibirin White Island a kasar New Zealand, inda tsauni yayi aman wuta na bazata. AFP Photo/Handout
Talla

Yan Sandan na New Zealand sun ce kimanin masu yawon bude ido 50 ne ke ziyartar tsibirin na White Island lokacin da wani sashi na tsaunin ya tarwatse bayan soma aman wutar.

Jami’an sun ce akalla mutane 24 ake fargabar sun halaka, yayinda wasu 23 suka samu tsira da raunukan kuna, kawo yanzu kuma biyar daga ciki sun mutu.

A halin yanzu dai jami’an agaji sun fitar da ran ceto wasu karin mutanen da aman wutar dutsen ya rutsa da su, bayan shafe tsawon lokaci ana lalube da jirage masu saukar ungulu.

Tsibirin White Island da aka fi sani da Whakaari, shi ne yankin dake kan gaba wajen fuskantar aman wutar dutse a kasar New Zealand, wanda kididdiga ta nuna cewar, akalla masu yawon bude ido dubu 10 ke ziyartar tsibirin duk shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.