Isa ga babban shafi
Faransa

Malaman Faransa sun kaurace wa azuzuwa

Malaman makarantun Faransa sun kaurace wa azuzuwa a karo na biyu cikin mako guda a daidai lokacin da ake ci gaba da zanga-zangar nuna adawa da sauye-sauyen tsarin biyan kudaden fansho da gwamnatin Emmanuel Macron da bullo da shi.

Wani bangare na masu zanga-zanga a birnin Paris na Faransa
Wani bangare na masu zanga-zanga a birnin Paris na Faransa REUTERS/Eric Gaillard
Talla

A halin yanzu babu alamar wannan zanga-zanga za ta kawo karshe, lura da cewa kwanaki shida kenan da masu boren ke fantsama kan tituna.

Zanga-zangar ta fi kamari a birnin Paris, inda akalla kashi 35 na malaman makarantun boko suka kaurace wa ayyukansu kamar yadda Ministan Ilimi Jean Michel Blanquer ya sanar.

Kazalika, bangaren sufuri a birnin na Paris na ci gaba da kasancewa a durkushe, lura da cewa, hanyoyin jiragen kasa guda biyu kadai ne ke aiki kamar yadda aka saba , yayin da aka rufe sauran hanyoyin, kana aka soke zirga-zigar jiragen sama da dama.

Ana kallon wannan boren a matsayin mafi muni da Kungiyar Kwadagon Faransa ta shirya tun bayan darewar shugaba Macron kan karagar mulki a shekarar 2017, inda ya yi alkawarin inganta tattalin arzikin kasar.

Shugabannin Kwadagon kasar sun lashi takobin ci gaba da gudanar da zanga-zanagarsu har nan da bikin Kirismati.

Sama da mutane dubu 800 suka fito a ranar farko ta fara gudanar da wannan zanga-zanga a sassan kasar ta Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.