Isa ga babban shafi
Birtaniya

Majalisar Birtaniya ta amince da yarjajeniyar ficewar kasar daga EU

Majalisar Birtaniya ta kada kuri’ar amincewa da kunshin yarjejeniyar ficewar kasar daga Tarayyar Turai wadda za ta kawo karshen takaddamar tsawon watanni kan makomar alakar kasar da kungiyar Tarayyar Turai a nan gaba.

Majalisar Birtaniya.
Majalisar Birtaniya. UK Parliament/Jessica Taylor
Talla

Rinyajen kuri’u 358 da Firaminista Boris Johnson ya samu a Majalisar zai bashi cikakkiyar damar ganin ya fitar da kasar daga Tarayyar Turai nan da ranar 31 ga watan Janairun sabuwar shekara.

Ka zalika kuri’ar ta yau Juma’a za ta kawo karshen tantamar Birtaniya da sauran takwarorinta kasashen turai 27 da ke kungiyar ta EU game da makomar kasuwancinsu.

Zaben makon jiya dai ya baiwa Firaminista Boris Johnson gagarumin rinjayen kujeru 365 daga cikin 650 da ke Majalisar kasar matakin da ke shirin tabbatar da kudirinsa na ganin kasar ta kammala ficewa daga EU nan da ranar 31 ga watan Janairu.

A ranar 9 watan Janairu ne Majalisar za ta sake kada kuri’a kan shirin na Johnson game ficewar Birtaniyar daga EU, kuri’ar da ake fatan ta zama ta karshe kan shirin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.