Isa ga babban shafi

Ghosn ya jaddada cewa bai aikata laifi ba

Tsohon shugaban kamfanin Nissan, Carlos Ghosn, ya jaddada cewa bai aikata laifi ba, inda yace ya tsare kasar japan ne saboda take hakkinsa na dan adam.Ghosn wanda ya yi jawabi karon farko, tun bayan tserewarsa daga Japan zuwa Beirut, ya bayyanawa dimbin 'yan jaridu dalilansa na kin fiskantar shara’a a Japan.

Tsohon shugaban hadakar kamfanin Nissan da Renault Carlos Ghosn.
Tsohon shugaban hadakar kamfanin Nissan da Renault Carlos Ghosn. REUTERS/Mohamed Azakir
Talla

Carlos Ghosn mai shekaru 65, da haihuwa, shugaban babban kamfanin masana'antar kera motoci na Nissan, ya isa kasar ta Lebanon kusan makwanni biyu da suka gabata, a cikin wani yanayi na ban mamaki.

Batun tserewan Ghosn ya fusata gwamnatin kasar Japan, wacce ta kira tserewarsa na rashin " gaskiya ne",

Sai dai Ghosn ya musanta zargin aikata laifi, ya kuma tsere ne daga zargin almubazzaranci da kudade da suka hada da biyansa diyyar dala miliyan 85, sakamon rashin adalci da cin zarafi da mahukuntar kasar ke masa.

Da yawa sunyi fatan Ghosn zai bayyana dalla-dalla yadda ya dare jirgin daga Japan zuwa Beirut ta hanyar Istanbul - labari mai ban mamaki.

Amma Ghosn ya shaida wa manema labarai cewa "ba yana nan ne don tattaunawa" game da yadda ya tsere daga Japan ba, sai dai ya fayyace dalilin fitcewarsa.

A cewar kafafan yada labarai na kasar ta Japan, Ghosn ya fice daga gidansa a Tokyo, ya hau jirgin kasa zuwa Osaka sannan kuma ya shiga jirgin sama zuwa Istanbul, ya kuma kaucewa jami'an shige da fitce, ta hanyar buya cikin akwati, kafin ya isa Beirut a ranar 30 ga Disamba.

Kamfanin Nissan ya ci gaba da nacewa yana da "tabbataccen shaida game da wasu munanan ayyuka da Ghosn ya yi".

Amma tawagar lauyoyin Ghosn daga Faransa ta tayi raddi sa'o'i kadan kafin ya fara taron manema labaru.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.