Isa ga babban shafi
Ingila

Sarauniyar Ingila ta tube sarautar Yarima Harry da Meghan

Tubabben yariman Ingila Harry da matarsa Meghan sun fara rayuwa kamar kowanne farar hula a Birtaniya bayan tube musu mukamin sarautar da Sarauniya Elizabeth ta yi a karshen makon jiya, yayinda ma’auratan za su biya masarautar fam miliyan 2 da rabi na kudaden harajin al’umma da aka yi amfani da su wajen gyaran gidansu na Frogmore da ke Windsor.

Sarauniyar Ingila, Queen Elizabeth II tare da Yarima Harry da matarsa.
Sarauniyar Ingila, Queen Elizabeth II tare da Yarima Harry da matarsa. Tolga AKMEN / AFP
Talla

Baya ga tube shi daga matsayin mai rike da Sarauta tsohon yariman na Ingila Harry ya kuma ajje mukaminsa na Soja da ma’aikatar tsaron Birtaniya ta bashi bayan halartarsa yaki har sau biyu cikin rundunar Sojin kasar zuwa Afghanistan.

Harry da matarsa Meghan ‘yar Canada bisa umarnin sarauniyar Ingila sun mika duk wani kayakin sarauta ciki har da masu hidimta musu, bayan wata ganawa tsakanin kusoshin masarautar da ya dauki tsawon lokaci.

A ranar 8 ga watan Janairun nan ne dai dambarwar gidan sarautar ta Ingila ta faro, bayan da Yarima Harry da matarsa Meghan tsohuwar ‘yar film a Amurka suka tsara sauya matsuguni daga Ingilar zuwa Canada ba tare da neman izinin Sarauniya Elizabeth ba.

Rahotanni sun bayyana cewa Harry da Meghan tsohuwar ‘yar film a Amurka sun yi kokarin shawo kan Sarauniyar mai shekaru 93 bayan yanke matakin ajje mukamin sarautar kwatankwacin yadda mahaifiyarsa Diana ta yi bayan rabuwa da yarima Charles a shekarar 1996.

Penny Junor shi ne marubucin tarihin masarautar Ingila, ya bayyana haihuwar Harry ga masarautar ta Ingila a matsayin babban kuskuren da bazai kankaru ba, yana mai bayyana shi a wanda babu cikakken jinin sarauta a jikinsa, bayan matakinsa na ajje mukamin da yace babban kuskure ne da bazai yiwa al’ummar Birtaniya dadi ba.

A baya-bayan nan dai Harry da Meghan sun yi kalamai da ke tuhumar masarautar ta Ingila game da mutuwa gimbiya Diana, batun da bai yiwa masarautar dadi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.