Isa ga babban shafi
Faransa

Faransawa sun sabunta zanga-zangar adawa da dokar fansho

Dubban Faransawa sun amsa kiran kungiyoyin kwadago kan soma gagarumar zanga-zanga ta musamman a yau Juma’a, don ci gaba da nuna adawa da sabon tsarin biyan kudaden fansho gwamnatin kasar.

Dubban faransawa a daren ranar alhamis yayin shirin soma gagarumar zanga-zangar adawa da sabuwar dokar fansho. 23/01/2020.
Dubban faransawa a daren ranar alhamis yayin shirin soma gagarumar zanga-zangar adawa da sabuwar dokar fansho. 23/01/2020. FRANCE 24
Talla

Matakin kungiyoyin kwadagon na zuwa ne bayan numfasawar da harkokin yau da kullum suka yi a sassan kasar ta Faransa, bayan shafe makwanni 7 suna yajin aikin da ya kassara fannoni daban daban musamman sashin sufuri, kan neman soke sabuwar dokar fanshon.

Zanga-zangar gami da yajin aiki na gudana ne a daidai lokacin da shugaban Faransa Emmanuel Macron ta hannun Fira Minista Edouard Phillipe ke gabatar da kunshin kwaskwarimar da ya yiwa tsarin biyan kudaden fanshon kasar ga majalisar ministoci a hukumance.

Daga majalisar ministoci ne kuma fadar shugaban kasar za ta aiki da kunshin sauye-sauyen zuwa ga majalisa domin tafka muhawara akai daga ranar 17 ga watan Fabarairu.

Wata kuri’ar jin ra’ayi da aka gudanar a baya bayan nan ta nuna cewar akalla kashi 61 na Faransawa ne ke goyon bayan janye sabuwar dokar Fanshon.

Sashin dokar fanshon da ya fusata kungiyoyin kwadagon Faransa dai shi ne karin shekarun ritaya daga 62 zuwa 64 da kuma banbanta adadin kudaden da za a biya wadanda suka zabi ajiye aiki a shekarun. Sai kuma hade wasu kamfanonin kula da kudaden fanshon zuwa wuri guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.