Isa ga babban shafi
fr

Erdogan ba ya mutunta alkwarin da ya dauka a Berlin - Macron

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya zargi Shugaban Turkiyya da rashin mutunta alkawuran da ya dau a zaman taron BerlinShugaban na Faransa na magana ne a wata ganawa da yayi da Ministan kasar Girka a Faransa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron Reuters
Talla

A  Laraban nan Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya zargi Shugaban Turkiyya Recep Tayip Erdogan da rashin mutunta sharudan da aka gindaya don samar da zaman lafiya biyo bayan aikewa da jiragen ruwan Turkiyya zuwa Syria don daukar dawainiyar yan ta’adda zuwa Libya.

Macron ya bayyana cewa a yan kwanakin nan rahotanni na nuni da cewa Turkiyya ta aike da jiragen ruwan ta zuwa Syria kuma yin haka daga Turkiyya ya sabawa alkawuran da Shugaban na Turkiyya ya dauka a zaman taron Baline.

Shugaba Macron ya bayyana goyan bayan sa matuka ga kasashen Cyprus da Girka, yana mai cewa take-taken Turkiya ya soma tadda hankulan wasu daga cikin kasashe musamman biyo bayan yarjejeniyar da Turkiyya ta kulla da gwamnatin hadin kan kasar Libya na dafa mata da sojan haya.

Shugaban Faransa a wata ganawa da yayi da Ministan kasar Girka a fadar Elysee ya sanar da cimma yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin Faransa da Girka da zata kai kasashen biyu ga kulla hulda ta fuskar dafa wa juna ta hanyar tsaro, wanda hakan zai baiwa Faransa damar girke dakarun ta na ruwa a Girka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.