Isa ga babban shafi
Faransa

Macron na shirin fayyace manufofin siyasarsa a Ketare

A ranar asabar mai zuwa, shugaban Faransa Emmanuel Macron, zai fayyace wasu daga cikin manufofinsa na siyasar ketare, tare da yin karin bayani a game da batutuwan da suka shafi siyasar tsaro ta Faransa.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa.
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa. REUTERS/Gonzalo Fuentes
Talla

A ranar ta asabar mai zuwa Emmanuel Macron zai gabatar da jawabi gaban taron kasa da kasa kan sha’anin tsaro a birnin Munich, yayin da zai yi amfani da wannan dama don ganawa da manyan ‘yan siyasa na kasar Jamus.

Tun farkon wannan shekara ne shugaban na Faransa ya kaddamar wani yunkuri da nufin warware sabanin da ke tsakaninsa da wasu kasashen na Turai a game da batutuwan da suka shafi tsaro da kuma manufofin ketare.

Bayan gabatar da jawabin, Macron zai ware wani lokaci don karba tambayoyi daga mahalarta taron, daga nan zai kara fayyace fatan da yake da shi ga kungiyar Turai, da rawar da kasar ke takawa a yankin Sahel da kuma alakar Faransa da Rasha.

A gefen wannan taro an tsara ganawa ta musamman tsakanin Emmanuel Macron da shugabannin jam’iyyar masu fafutukar kare muhalli a Jamus wato Robert Habeck da kuma Annalena Baerbock.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.