Isa ga babban shafi

Wani dan wasan Dortmund yafi Messi da Ronaldo cin kwallo

Matashin dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Bourussia Dortmund mai shekaru 19, Erling Haaland ya kafa tarihi wajen nuna nuna bajinta zura kwallaye a duniyar tamola.

Dan wasan gaba na kungiyar Borussia Dortmund Erling Haaland
Dan wasan gaba na kungiyar Borussia Dortmund Erling Haaland © REUTERS/Leonhard Foeger
Talla

Erling Haaland, ya yi nasarar zura kwallaye biyu a wasan da ya baiwa kungiyarsa ta Borussia Dortmund nasara kan PSG a wasar da suka kara a zagaye na biyu na gasar zakarun Turai a daren Talata.

Yanzu haka dan wasan nada kwallaye 39, kuma sau shida yake cin kwallaye 3 a wasa daya da ake kira hat-trick.

Ya ciwa Borussia Dortmund Kwallaye 11 cikin wasanni bakwai, kana kwallaye 10 a wasanni 7 na gasar zakarun Turai, duk wadannan a shekaru 19 kachal.

Irin nasarori da wannan matashi ke samu Messi da Ronaldo duk basu yi a wannan kaka ba.

Dan wasan ne yafi kowa yawan kwalleye a gasar zakarun Nahiyar Turai tsakanin shekarar 2019 – 2020, wato fiye ma da kwallayen kungiyar Barcelona baki daya a gasar.

Haaland shine dan wasan farko a kungiyar Dortmund da ya kafa tarihi zura kwallo a wasansa na farko a gasar Bundesliga, da ma gasar neman Kofin kalubale na Jamus.

Haka zalika, shine dan wasan Dortmund na farko da ya taba cin kwallo a wasan sa na farko a gasar zakarun Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.