rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Uganda Kwallon Kafa Eritria

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

‘Yan wasan Eritrea sun nemi mafakar Siyasa a Uganda

media
Eritreansanye da Duruwan kaya a lokacin da suke wasa da 'Yan wasan Kenya cecafafootball.org

‘Yan wasan kasar Eritrea da suka yi batan dabo yanzu haka sun nemi samun izinin mafaka a kasar Uganda maimakon komawa gida. kamar yadda Karamin Ministan ‘yan gudun hijira Musa Ecweru yace ‘yan wasan su 18 sun shaida masu ba za su koma kasarsu ba don haka suna neman mafakar siyasa don komawa ba zai Haifa masu da mai ido ba.  


Kuma Ministan ya tabbatar da cewa ‘yan wasan suna hannun Gwamnatin Uganda cikin koshin lafiya.

Rahotanni sun ce wannan ne karo na hudu da ‘yan wasa ke yin layar zana. Kuma ana ganin sun gudu ne saboda tsira daga mulkin danniya da ake yi a kasashensu.

A shekarar 2007, wasu ‘Yan wasan Eritrea 12 sun taba neman mafaka a kasar Kenya haka ma wasu ‘Yan wasa 13 sun taba neman mafaka a Tanzania.

Kawo yanzu dai mahukuntan Eritrea basu ce komi ba game da salwantar su.