Isa ga babban shafi
Wasan Tennis

Azarenka ta kare kofinta na Qatar Open, bayan doke Serena Williams

Victoria Azarenka, ‘yar kasar Belarus ta doke Serena Williams a wasan karshe na gasar Qatar Open, inda ta lallasa ta da ci 7-6, (8-6) 2-6, da kuma 6-3, kuma wannan shine karo na biyu da Azarenka ke samun damar doke Williams a haduwa goma sha uku da su ka yi, wanda ya sake bata damar kare kofin gasar ta Qatar Open.

Victoria Azarenka
Victoria Azarenka Reuters
Talla

Williams, yar shekaru 31, kuma ‘yar kasar Amurka a daya bangaren ta samu damar kare kofinta na Australian Open da aka kammala a kwana-kwanan nan.

A yanzu haka burinta shine ta wanke kayin da ta sha a gasar Dubai Open da za a fara a kwanan nan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.