Isa ga babban shafi
Tennis

Li na ta fice French Open

Li na ta China ta fice gasar French Open ta Roland Garros da ake gudanarwa a Faransa, bayan ta sha kashi a hannun Bethanje ta Amurka a zagaye na biyu. Wannan ne kuma karo na farko da Li na ta fice tun a zagaye na biyu, bayan ta lashe kofin gasar a shekarar 2011.

Li Na 'Yan wasan Tennis ta China
Li Na 'Yan wasan Tennis ta China REUTERS/Damir Sagolj
Talla

Samantha Stosur da kuma Jelena Jankovic dukkaninsu sun tsallake zuwa zagaye na uku duk da ruwan sama da ya kawo tsaiku a lokacin da suke karawa.

Stusor ta Australia dai ta doke Kristina ce ta Faransa a yayin da kuma Jankovic ta doke Muguruza ta Spain

A bangaren maza, Rafeal Nadal wanda ke harin lashe kofin gasar karo na 8 ruwan sama ya kawo tsaikun karawar shi da dan wasan Slovakia Martin Klizan, Kamar yadda shi ma zakaran Tennis na duniya Novak Djokovic, ruwa ya kawo tsakun karawar shi da dan wasan Argentina Pello da yammacin Alhamis.

‘Yan uwan juna kuma Serena da Venus Williams za su fice daga karawar kawance ta mutane biyu a gasar French open, saboda raunin da Venus ta samu a bayanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.