Isa ga babban shafi
Tennis

Nadal ya sha kashi a Wimbledon

Rafael Nadal ya fuskanci bacin rana a Wimbledon bayan ya sha kashi a hannun dan wasan Belgium Steve Darcis a karawar farko. A bara ma tun a zagayen na biyu ne Nadal ya sha kashi a hannun Lukas Rosol na jamhuriyyar Czech.

Rafael Nadal a lokacin da ya sha kashi a Wimbledon.
Rafael Nadal a lokacin da ya sha kashi a Wimbledon. REUTERS/Stefan Wermuth
Talla

Duka ba da jimawa ba ne Rafael Nadal ya lashe kofin Rolland Garrso karo na 8. Kodayake dan wasan yace Filin Rolland Garros ya banbanta da filin Wimbledon.

Yanzu dai hammaya ta dawo ne tsakanin Andy Murray da Roger Federer da kuma Novak Djokovic.

Andy Murray na Birtaniya ya tsallake zuwa zagaye na biyu bayan ya doke dan wasan Jamus Benjamin Becker, a zagaye na uku kuma zai kara ne da dan wasan Taiwan wanda ya doke shi a wasannin Olympics da aka gudanar a 2008.

Roger Federer ya fara farautar lashe kofin Wimbledon karo na 8 inda ya tsallake zagaye na biyu bayan ya lallasa Victor a dai dai lokacin da ya yi bukin cika shekaru 10 da fara lashe kofin farko.

A bangaren mata Sara Errani ta Italiya ita ce ta fara shan kashi cikin manyan jaruman Tennis inda matashiya Monica ta lallasa ta 6-3, 6-2.

Sharapova da Azerenka da Caroline Wozniacki, Ana Ivanovic da Jelena Jankovic dukkaninsu sun tsallake zuwa zagaye na biyu.

A yau ne kuma za’a kwashi kallo inda Serena Williams za ta fara karawa tsakaninta da Mandy Minella ta Luxembourg, haka kuma Zakaran Tennis na Duniya Novak Djokovic a yau ne zai fara fafatawa tsakanin shi da Florian Mayer na Jamus wanda Djokovic ya doke a bara zagayen Kwata Fainal.

Dukkaninsu dai za su yi fatar kaucewa annobar da ta shafi Nadal, musamman Serena da ta lashe kofin Rolland Garros.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.