Isa ga babban shafi
Tour de France

Froome ya nisanta kan shi da Armstrong

Dan tseren keken Birtaniya Chris Froome ya yi watsi da zargin da ake ma shi cewa zai iya bin sahun zakaran tseren keke Lance Armstrong wanda aka kwace wa nasororin shi guda bakwai saboda ya kwankwadi kwayu masu sa kuzari.

Christopher Froome a tserene keken gasar Tour de France
Christopher Froome a tserene keken gasar Tour de France REUTERS/Jean-Paul Pelissier
Talla

Dan wasan yace Armstrong ya ci amana amma shi na yana tsere ne na tsabta
A ranar Lahadi, Dan wasan ya ci gaba da jan ragamar gasar na mallakar doruwra riga bayan ya lashe tseren keken hawa tsauni a karo na 100 da ake gudanar da gasar.

Wani batun kuma shi ne inda Chris Froome yace yafi kaunar a kira shi baturren Birtaniya duk da cewa a Afrika ne aka haife shi kuma a nan ne ya girma.

A kasar Kenya ne aka haifi Froome kafin ya koma Afirika ta kudu inda ya girma. Dan wasan ya tsallake zuwa Birtaniya ne a 2008 saboda nan ne tushen iyayaen shi.

Amma duk da haka dan wasan bai taba zuwa Birtaniya ba sai a 2007, kuma gasar tseren keke ce ta kai dan wasan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.