rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kwallon Kafa Ecuador

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Benitez na Ecuador ya mutu a Qatar

media
Christian Benitez dan wasan kasar Ecuador da ya mutu yana da shekaru 27 REUTERS/Gary Granja

Wani dan wasan kasar Ecuador Christian Benitez ya mutu yana da shekaru 27 a kasar Qatar sanadiyar bugun zuciya a jiya Litinin. Dan wasan na kungiyar El-Jaish ta Qatar ya Mutu ne bayan an kwashe shi zuwa Asibiti.


Benitez tsohon dan wasan Birmingham City ne ta Ingila, kuma kungiyar El-Jaish tace dan wasan yana cikin ‘yan wasanta da suka buga mata wasa a ranar Lahadin da ta gabata kafin matsalar ta same shi.