Isa ga babban shafi
CAF

Eritrea ta fice wasannin neman shiga gasar cin kofin Afrika

Kasar Eritrea ta fice daga cikin wasannin neman shiga gasar cin kofin Afrika da za’a gudanar a badi, kamar yadda masu shirya gasar suka fitar da sanarwa ba tare da wani bayani akan dalilin ficewar kasar daga gasar ba.

'Yan wasan kwallon kafa na kasar Eritrea sanye da bular riga
'Yan wasan kwallon kafa na kasar Eritrea sanye da bular riga DR
Talla

Amma wata kila dalilin ba ya rasa nasaba da yadda ‘yan wasan Eritrea ke yin amfani da damar na kin komawa kasarsu idan sun fita buga wasa da wata kasa.  Akwai ‘Yan wasan Eritrea guda 9 da suka yi batan dabo a kasar Kenya a watan Disemba a lokacin da suka je buga wasa a kasar.

Wasunsu suna cewa saboda kuncin rayuwa ne, a karamar kasar da ta samu ‘yancin kai daga kasar Habasha shekaru 21 da suka gabata.

A watan Afrilu an hada Eritrea wasa ne da kasar Sudan ta kudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.