rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Ingila Renon Ingila

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Wasannin renon Ingila a rana ta Bakwai

media
Brianne Theisen-Eaton ta Canada ta sha gaban 'yar uwarta Jessica Zelinka a tseren gudun mita 200 a wasannin kasashen renon ingila da ake gudanarwa a Scotland REUTERS

A yau Laraba aka shiga rana ta bakwai a wasannin kasashen renon Ingila da ake gudanarwa a birnin Glasgow a kasar Scotland, inda a yau za’a fafata a tseren gudun mita 400 a bangaren Maza da mata. Kasar Australia ce ke kan gaba da yawan zinari da jimillar lambobin yabo 101, yayin da Ingila ke bi mata da jimilla 93.


Kasar Canada ce matsayi na uku.

Kasar Afrika ta kudu ce a sahun gaba a Kasashen Afrika da ke haskawa a wasannin, amma ta bakwai da yawan lambobin yabo 26 a jerin kasashen renon Ingila da ke fafatawa.

Kasar Kenya tana matsayi na 10 da yawan lambobin yabo 9. Najeriya tana matsayi na 12 ne, da yawan zinariya 6 tagulla uku, azurfa 5, jimilla 14.