Isa ga babban shafi
Faransa

An haramtawa Ibrahimovic wasanni 4

Hukumar kwallon League 1 a Faransa ta haramtawa Zlatan Ibrahimovic buga wasanni hudu a gasar saboda wasu kalaman da basu yi wa hukumar dadi ba da dan wasan ya furta na sukar alkalan wasa.

Mchezaji wa PSG, Zlatan Ibrahimovic akijiuliza iwapo kwenda sare ya bao 1-1 dhidi ya Chelsea ni matokeo mazuri kwa timu yake.
Mchezaji wa PSG, Zlatan Ibrahimovic akijiuliza iwapo kwenda sare ya bao 1-1 dhidi ya Chelsea ni matokeo mazuri kwa timu yake. REUTERS/Christian Hartmann
Talla

Ibrahimovic ya ce bai kamata PSG mai manyan ‘yan wasa tana buga kwallo a Faransa ba saboda yadda ake kin kungiyar musamman alkalan wasa.

Akan haka Dan wasan na Sweden zai kauracewa wasan da PSG za ta buga da Nice da Lille da Mets da kuma Nantes, saboda kalamansa.

Shugaban hukumar gasar league 1 a Faransa ya ce kalaman Ibrahimovic rashin da’a ne da kuma cin mutunci ne ga Faransawa.

Hukuncin dai na zuwa ne bayan dan wasan ya jefa kwallaye uku a ragar Saint Etienne a gasar kalubale ta Faransa a ranar Laraba.

Ibrahimovic kuma zai kauracewa wasan Barcelona a makon gobe saboda jan katin da ya karba a karawarsu da Chelsea a gasar zakarun Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.