Isa ga babban shafi
Rolland Garros

Nadal na harin lashe kofi na 10 a Faransa

Rafael Nadal ya tsallake zuwa zagaye na biyu a gasar Roland Garros da ake gudanarwa a Faransa bayan ya doke Quentin Halys a fafatawarsa ta farko inda ya ke harin lashe kofin gasar karo na 10.

Rafael Nadal ya doke Quentin Halys a Roland Garros
Rafael Nadal ya doke Quentin Halys a Roland Garros Photo: René-Worms / RFI
Talla

Karo na 67 ke nan da Nadal ke samun nasara a gasar Roland Garros, amma akwai yiyuwar Nadal zai hadu da jarmumin Tennis din na duniya Novak Djokovic a zagayen kwata fainal.

Nadal na fuskantar kalubale bayan ya shafe lokaci a bana ba tare da ya lashe kofin gasar Tennis da ake gudanarwa a turda ba, kusan tun a 2005.

A zagaye na biyu Nadal zai hadu ne da takaransa na Spaniya Nicolas Almagro ko kuma Alexandr na Ukraine.

Djokovic na harin lashe kofin Roland Garros ne a karo na farko wanda shi ne kofin da bai taba lashe wa ba cikin manyan gasannin Tennis na duniya.

Bangaren Mata

Petra Kvitova da ta lashe kofin Wimbledon, ta doke Marina Erakovic, yanzu kuma Kvitova za ta hadu ne da Soler Espinosa ta Spain.

Tsohuwar jarumar tennis ta duniya Caroline Wozniacki ta kai zagaye na biyu bayan ta doke Karin Knapp ta Italiya.

Idan an jima ne babba Jarumar tennis ta duniya Serena Williams za ta fara fafatawa a gasar inda zata kara da Andrea Hlavackova.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.