Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Chile ta lashe Copa America

Al’ummar kasar Chile sun gudanar da biki a Santiago tare da kofin da suka lashe na gasar Copa America bayan sun doke Argetina ci 4 da 1 a bugun fanariti a ranar Assabar.

'Yan wasan Chile sun yi biki a fadar gwamnatin kasarsu bayan sun lashe Copa America
'Yan wasan Chile sun yi biki a fadar gwamnatin kasarsu bayan sun lashe Copa America REUTERS/Carlos Garcia Rawlins
Talla

An dai shafe mintina 120 babu wanda ya zira kwallo a raga a karawar kasashen biyu.
Wannan ne karon farko da Chile ta lashe kofin a tarihin Copa America bayan ta doke Argentina.

Chile ta lashe kofin ne bayan ‘Yan wasan Argentina biyu sun barar da Fanariti.

Wasu dai na ganin Messi ne ya yi hasarar kofi a bana ba Argentina ba wanda aka dade ana danganta shi da Maradona a kasar, amma har yanzu bai lashewa kasar wani babban kofi ba.

watanni 12 ke nan da Jamus ta haramtawa Messi lashe kofin duniya a Brazil, yanzu kuma Chile ta haramta ma shi Copa America.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.