rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Renon Ingila Wasanni Afrika ta kudu

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Birnin Durban zai karbi bakuncin wasanin kasashen renon Ingila a 2022

media
Birnin Durban, na Afrika ta kudu AFP PHOTO / GIANLUIGI GUERCIA

Birnin Durban na Afrika ta kudu ya samu damar daukar nauyin wasannin kasashen renon Ingila, wanda ya kasance gari na farko daga Afrika da zai karbi bakuncin Wasannin a 2022.


Birnin Durban ya samu nasarar karbar bakuncin wasannin ne bayan birnin Edmonton na Canada ya janye takararsa a watan Fabrairu.

Al’ummar Afrika ta kudu musamman mutanen birnin Durban sun yi biki akan nasarar da suka samu na karbar bakuncin wasannin na kasashen renon Ingila da za a gudanar karo na 85.

A shekarar 1930 ne aka soma wasannin da ake gudanartwa duk bayan shekaru 4, kuma wannan ne karon farko da za a gudanar da wasannin a Afrika.

Za a bude wasannin ne a ranar haihuwar tsohon shugaban Afrika ta kudu Nelson Mandela wato 18 ga watan Yuli na 2022.