Isa ga babban shafi
IAAF

Hukumar WADA ta bukaci a dakatar da Rasha

Rahoton binciken hukumar yaki da shan kwayu masu sa kuzari a wasannin guje guje da tsalle tsalle WADA, ya bukaci a dakatar da hukumar wasannin guje guje da tsalle tsalle ta Rasha saboda rashin daukar matakan magance girman matsalar shan kwayu masu sa kuzari tsakanin ‘Yan wasan kasar.

Shugaban Hukumar guje guje da tsalle tsalle Sebastian Coe
Shugaban Hukumar guje guje da tsalle tsalle Sebastian Coe REUTERS/Jason Lee
Talla

Rahoton hukumar ya gudanar da kwakkwaran bincike tare da nazari akan ayyukan shan kawyu masu sa kuzari a Rasha.

Rahoton wanda aka gabatar a jiya Litinin ya bukaci A haramta wa wasu ‘Yan wasan Rasha guda 5 shiga harakar wasanni na har abada wadanda suka hada da Mariya Savinova ‘Yar tseren gudun mita 800, kan zargin karin kuzari. Rahoton ya ce an yi wa wasannin Olympic da aka gudanar 2012 a London zagon kasa saboda kasancewar ‘yan wasan na Rasha.

Matakin dai zai haramtawa Rasha shiga wasannin Olympic a badi.

Rahoton kuma ya bukaci hukumar wasannin guje guje da tsalle tsalle IAAF ta yi nazari akan cancantar Rasha na karbar bakuncin wasannin matasa a 2016.

Rahoton ya zayyana hujjoji akan zarge zargen na Rasha, inda rahoton yace babu wani gwaji da hukumar wasannin kasar ke gudanarwa akan karin kuzari.

Shugaban hukumar wasannin guje guje da tsallae Sebastian Coa yace Rasha tana da dama daga nan zuwa Juma’a ta kare kanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.