Isa ga babban shafi
Wasanni

Chiellini zai yi jinyar kwanaki 20

Dan wasan baya na kiungiyar kwallon kafa ta Juventus, Giorgio Chiellini ba zai samu damar taka leda ba har na tsawon kwanaki 20 sakamakon raunin da ya samu a kafarsa ta dama kamar yadda kungiyar ta sanar a jiya Talata. 

Giorgio Chiellini da Joel Campbell
Giorgio Chiellini da Joel Campbell REUTERS/Brian Snyder
Talla

Yanzu haka, Chiellini ya shiga sahun yan kungiyar da ke jinya da suka hada da Sami Khedira da Martin Caceres, kuma ba zai buga wasan da Juventus za ta yi da Napoli ba a ranar asabar mai zuwa.

Sannan kuma mawuyaci ne ya samu damar buga wasan da za su yi da Bayern Munich a zagayen farko na kungiyoyi 16 da suka kai zagayen gaba a gasar cin kofin zakarun Turai.

A ranar 23 ne ga wanann watan na Fabairu Juventus  za ta  kara da Bayern Munich.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.