Isa ga babban shafi
Wasanni

Nadal ya goyi bayan a hukunta Sharapova

Gwarzan dan wasan kwallon Tennis, Rafael Nadal ya kare salon da ya ke amfani da shi wajen samun horo, yayin da ya musanta zargin da ake yi masa cewa, ya taba shan kwaya mai kara kuzari da aka haramta wa 'yan wasa.

Gwarzan dan wasan Tennis Rafael Nadal
Gwarzan dan wasan Tennis Rafael Nadal Reuters/Vincent Kessler
Talla

Nadal wanda ya zanta da manema labarai a gasar Wells ta kasar India game da kwayar da Maria Sharapova ta kwankwada ya ce, ya kamata a hukunta ta akan wannan laifin da ta aikata.

Fitacciyar 'yar wasan ta Tennis dai ta fasa kwai da kanta, inda ta sanar da duniya cewa tana shan daya daga cikin kwayoyin da aka haramta wa 'yan wasa, lamarin da ya sa kamfanonin da ke hulda da ita suka katse alakarsu da ita.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.