Isa ga babban shafi
Wasanni

PSG ta yi waje da Chelsea a gasar zakarun Turai

Kungiyar kwallon kafa ta PSG ta yi waje da Chelsea a gasar cin kofin zakarun Turai bayan ta doke ta da ci 2-1 a jiya Laraba.

Dan wasan PSG Zlatan Ibrahimovic ya taka rawar gani a fafatawarsu da Chelsea a jiya Laraba.
Dan wasan PSG Zlatan Ibrahimovic ya taka rawar gani a fafatawarsu da Chelsea a jiya Laraba.
Talla

Fitaccen dan wasan PSG Zlatan Ibrahimovic ya taka rawar gani a wasan na jiya domin shi ne ya taimaka wa Adrien Rabiot ya zura kwallo ta farko a minti na 16 da fara wasa.

Koda ya ke Diego Costa na Chelsea ya farke kwallon a minti na 27.

Amma gabanin a tashi wasa,Ibrahimovic ya ci wa PSG kwallo ta biyu a minti na 67.

Yanzu haka dai PSG ta samu nasarar tsallakawa zuwa zagayen wasan dab da na kusan karshe.

Itama Benfica ta samu nasarar kai wa matakin wasan dab da na kusan karshe bayan ta casa Zenith St. Petersburg da ci 2-1 a karawarsu ta jiya a gasar ta cin kofin zakarun Turai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.