Infantino na cikin bayanan sirrin Panama
Bayanan sirrin Panama da aka bankado sun shafi har da sabon shugaban hukumar FIFA Gianni Infantino wanda ya gaji Sepp Blatter da badakalar rashawa ta kawo karshen shugabancinsa.
Wallafawa ranar:
Takardun Panama sun kwarmata cewa Infantino ya sanya wa wasu kamfanonin Argentina biyu hannu kan samun ‘yancin haska wasannin gasar zakarun Turai da wasu wasannin a talebijin.
Mutanen da ke da mallakin kamfanonin biyu suna cikin wadanda Amurka ke zargi da badakalar rashawa a hukumar FIFA.
Rahoton Panama yace sanya hannun na Infantino ya sa mutanen biyu Hugo and Mariano Jinkis sun samu mugunyar riba domin sun saye ‘yancin ne akan kudi dala dubu 140 amma suka sayar akan kudi dala dubu 440.
Wannan dai na iya janyo a bude sabon bincike akan sabon shugaban hukumar ta FIFA.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu