rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kwallon Kafa French League

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sofiane Boufal na Morocco ya lashe Kyautar Marc-Vivien Foe ta RFI

media
Dan Morocco Sofiane Boufal. REUTERS/Jacky Naegelen

Dan wasan Morocco Sofiane Boufal da ke taka kwallo a Lille shi ne ya lashe kyautar Mar Vivien-Foe ta gwarzon dan wasan Afrika da ke taka kwallo a gasar Lig 1 ta Faransa.


Dan wasan ya doke dan kasar Senegal Chiek Ndoye da dan Algeria Rachid Ghezzal.

Tashar RFI da France 24 ne dai ke bayar da kyautar ga yan wasan kwallon kafa na Afrika a Faransa.

Sofiane ya jefa kwallaye 11 a wasanni 29.

Vincent Enyeama na Najeriya da ke tsaron gida a Lille  ya taba lashe kyautar ta Marc-Vivien Foe a 2014.