rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Gasar Cin Kofin Turai Faransa Iceland Portugal

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Iceland ta rike Portugal a gasar Euro 2016

media
Portugal da Iceland sun yi kunnen doki 1-1 a gasar Euro 2016 REUTERS/Jason Cairnduff Livepic

Tawagar kwallon kafa ta Iceland ta rike Portugal 1-1 a karawar da kasashen biyu suka yi a jiya Talata a wasan cin kofin nahiyar Turai da ake gudanarwa a Faransa.

 


Dan wasan Portugal mai suna Nani ya fara zura kwallo a minti na 31da fara wasa amma daga bisa Iceland ta farke ta hannun Bjarnason a minti na 50.

Sai dai Gwarzon dan wasan Portugal wanda ke taka Leda a Real Madrid, Christiano Ronaldo bai ji dadin yadda wasan ya kaya ba, kuma sau 10 yana dukan kwallo domin neman jefa ta a ragar Iceland amma hakan ya ci tura.

To sai dai duk da haka ya kafa tarihi, lura da cewa sau 127 kenan yana wakiltar kasarsa a gasa daban daban, abinda ya ba shi damar kamo Luis Figo wanda shi ma ya buga wa Portugal din wasanni har guda 127.

An yi zaton Iceland za ta sha kashi a hannun Portugal amma ta bayar da mamaki, kuma a karon farko kenan da ta shiga wata babbar gasa a tarihinta.

A ranar Asabar mai zuwa ne, Portugal za ta hadu da Austria yayin da Ronaldo ya yi

Ita ma Austrian ta sha kashi a hannun Hungary da ci 2-0 a fafatawar da suka yi jiya a filin wasa na Bordeaux a gasar ta Euro 2016.

Idan anjima ne kuma Romania za ta kece raini da Switzerland yayin da Faransa za ta kara da Albania, sai kuma Rasha wadda za ta hadu da Slovakia.