Isa ga babban shafi
Wasanni

Messi na Argentina ya kafa tarihi

Lionel Messi na Argentina ya kafa tarihi, inda ya kasance dan wasan da ya fi ci wa kasar kwallaye a tarihinta na tamaula.

Lionel Messi na Argentina da ke taka leda a Barcelona
Lionel Messi na Argentina da ke taka leda a Barcelona Reuters/Grigory Dukor
Talla

Messi ya kafa wannan tarihin ne a wasan da suka lallasa Amurka da ci 4-0 a gasar cin kofin Copa America, abinda ya bai wa Argentina damar tsallakawa zuwa matakin wasan karshe a gasar.

A minti na 32 da fara wasa ne, Lionel Messi ya zura kwallonsa ta 55 bayan an ba shi damar bugun tazara.

Tuni dai Amurka ta hada inata-inata domin komawa gida bayan wannan kashin da ta sha a gaban ‘yan kallo fiye da dubu 70 da suka taru a filin wasa na Houston NRG domin kallon wasan na jiya Talata.

A karo na farko kenan cikin shekaru 23 da suka gabata da kasar Argentina ke neman lashe gasar Copa America.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.