Belgium da Jamus da Faransa sun kai gaci a Euro 2016
Kasar Belgium ta samu nasarar tsallakawa zuwa matakin wasan dab da na kusan karshe a gasar cin kofin kasashen Turai da ake gudanarwa a Faransa bayan ta lallasa Hungary da ci 4-0 a fafatawar da suka yi jiya Lahadi.
Wallafawa ranar:
A karo na farko kenan da Belgium ta samu nasarar tsallawa zuwa wannan matakin tun lokacin da Jamus ta yamma ta doke ta wasan karshe a shekara ta 1980.
A bangare guda, a karon farko kenan da dan wasan Belgium Eden Hazarda ya ci kwallo a gasar ta Euro 2016 kuma yanzu haka kasar za ta hadu da Wales a birnin Lille da ke kan iya da Belgium da Faransa domin neman gurbi a matakin wasan dab da na karshe.
Itama kasar Jamus ta samu nasarar shiga matakin gaba na gasar ta Euro 2016 bayan da ta doke Slovakia da ci 3-0 a karawar da suka yi jiya a Lille.
A karo na farko kenan da Jerome Boateng ya ci wa Jamus kwallo a wata gasar kasa da kasa kuma shi ne ya fara zura kwallo a minti na 8 da fara wasan na jiya.
Sau 63 kenan da dan wasan ke wakiltan kasarsa a gasar kasa da kasa.
Ita ma Faransa mai masaukin baki ta samu shiga zagayen gaba, bayan da ta doke jamhuriyar Irelanda ci 2-1.
Yaznu haka, Faransa za ta hadu da Ingila ko kuma Iceland a filin wasa na Stade de France a ranar Litinin mai zuwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu